Iran Ta Aike Wa Da MDD Wasika Akan Kasar Canada

Jakadan Iran a MDD  Amir Sa’id Iruni ya aike da wasika zuwa ga babban sakataren MDD saboda yadda kasar Canada, ta bayyana dakarun kare juyin

Jakadan Iran a MDD  Amir Sa’id Iruni ya aike da wasika zuwa ga babban sakataren MDD saboda yadda kasar Canada, ta bayyana dakarun kare juyin musulunci na Iran a matsayin ‘yan ta’adda,tare da bayyana hakan a matsayin wanda ya sabawa doka,kuma abu mai hatsari da manufarsa siyasa ce.

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran wani sashe ne mai matukar muhimmanci na rundunar tsaron kasar Iran, don haka bayyana ta a matsayin ‘yan ta’adda ya sabawa doka.

Iruni ya zargi kasar ta Canada da yin abubuwa masu yawa da suke cin karo da dokokin kasa da kasa haka nan dokokin MDD.

Har ila yau, wakilin Iran din a MDD ya bayyana aniyar kasarsa na kai karar Canada a kotun duniya.

Jakadan na Iran a MDD ya kuma ce, wannan irin matsaya ta Canada, tana a karkashin halayyarta ta kiyayya ne da jamhuriyar musulunci ta Iran, kuma baraza ce ga zaman lafiya na sulhu na kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments