Iran: Sanya Sunan Dakarun IRGC A Cikin Jerin ‘Yan Ta’adda Hidima Ce Ga Isra’ila

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Canada ta dauka na sanya dakarun

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Canada ta dauka na sanya dakarun IRGc a cikin jerin ‘yan ta’adda, tare da bayyana hakan a matsayin bababr kyauta ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ‘yan ta’adda da makiya zaman lafiya da kwanciyar hankali a gabas ta tsakiya.

“Abin da kasar Canada ta yi na ayyana wani muhimmin bangare na rundunar sojan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ya taka rawar da ba za ta iya maye gurbinta ba wajen kare tsaron kasar Iran, da kuma kare tsaro da zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya, da kuma fuskantar kalubalen Ta’addancin Daesh, a matsayin ‘yan ta’adda, hakan da Canada ya kasance mai muni kuma ya saba wa ka’idoji da ka’idojin dokokin kasa da kasa,”

Bagheri Kani ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da aka buga a dandalin sada zumunta na X a ranar Alhamis.

Bagheri Kani ya ce gwamnatin Canada za ta dauki alhakin sakamakon wannan mataki na tunzura jama’a da kuma rashin gaskiya.

A wani mataki na nuna adawa da Iran, Ministan Tsaron kasar Canada Dominic LeBlanc Ottawa , ya sanya IRGC a matsayin “kungiya ta ta’addanci”.

A watan da ya gabata, Majalisar Dokokin Canada ta amince da wani kuduri wanda ke kira ga gwamnatin Firayim Minista Justin Trudeau da ta sanya sunan kungiyar IRGC tare da korar Iraniyawa kusan 700 daga kasar.

Matakin dai ya sa Canada ta zama kasa ta biyu a Arewacin Amurka, bayan gwamnatin da ta sanya IRGC cikin jerin ‘yan ta’adda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments