Kasashen Iran da Rasha da Turkiyya sun yi Allah wadai da cin zarafin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da yi a yankin yammacin Asiya, inda suka yi kira da a kara kokarin da kasashen duniya ke yi na ganin an tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza.
Bayan kammala taron kasa da kasa karo na 22 kan kasar Siriya na Astana, da aka gudanar a babban birnin kasar Kazakhstan, kasashen uku sun yi kakkausar suka da nuna matukar damuwarsu kan kisan gillar da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, da kuma hare-haren wuce gona da iri da Isra’ilar ke yi a zirin Gaza da Lebanon da Yammacin Kogin Jordan.”
Sun yi kira ga gamayyar kasa da kasa, musamman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da su samar da tsagaita bude wuta cikin gaggawa da kuma kai agajin jin kai ba tare da cikas ba a Gaza.
bangarorin sun kuma yi Allah wadai da hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a Syria, inda suka dauki irin wannan mataki a matsayin cin zarafin dokokin kasa da kasa.
Sanarwar ta hadin guiwa ta kuma jaddada mahimmancin dawo da tuntubar juna da kuma ci gaba da kokarin daidaita dangantakar dake tsakanin Ankara da Damascus.
Sun jaddada wajibcin yaki da ta’addanci, da saukaka komawar ‘yan kasar Siriya cikin aminci tare da kiran a samar musu da tallafi daga hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta UNHCR.