Iran: Mutane Da Dama Sun Fito Don Kada Kuri’unsu A Zaben Shugaban Kasa

Rahotanni da suke fitowa daga ma’aikatar cikin gida na kasar Iran sun bayyana cewa an kara lokacin zabe da sa’o’ii 2 saboda yawan mutane da

Rahotanni da suke fitowa daga ma’aikatar cikin gida na kasar Iran sun bayyana cewa an kara lokacin zabe da sa’o’ii 2 saboda yawan mutane da suka fito don kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa karo na 14 a kasar tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar shekaru 45 da suka gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar cikin gida tana fadar cewa mutane kimani miliyon 61 ne suka cancanci kada kuri’unsu a wannan zaben shugaban kasa, wanda aka gudanar kwanaki 40 kacal da shahadar marigayi shugaba Ibrahim Ra’isi.

Ahmad Wahidi ministan cikin gida ya bayyana cewa gudanar da zabe cikin kwanaki 40 kacal da rashin shugaban kasa ya nuna cewa tsarin da ke tafiyar da JMI yana tafiya kamar yadda ya dace, kuma baya fuskantar wata matsala.

Kakakin hukumar zaben kasar Mohsen Eslami ya bayyana cewa sun sami bukatar Karin lokacin kada kuri’a daga cibiyoyin zabe da dama a kasar, saboda yawan mutanen da suka fito don kada kuri’unsu. Don haka hukumar tare da hadin kai da ma’aikatar cikin gida sun tsaida shawarar kara sa’o’i biyu a zaben. Wato har zuwa karfe 8 na yamma maimakon karfe 6.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments