Iran: Masana A Iran Sun Kera Wata Na’ura Mai Muhimmanci A Aikin Tiyata A Cikin Gida Wanda Ya Kawo Sauki A  Aikin

Wani kamfanin kera kayakin likitanci mai zaman kansa ya sami nasarar kera wata na’ura wacce ake kira ‘bipolar surgical scissors’ wanda yake sawwaka aikin tiyata

Wani kamfanin kera kayakin likitanci mai zaman kansa ya sami nasarar kera wata na’ura wacce ake kira ‘bipolar surgical scissors’ wanda yake sawwaka aikin tiyata a aikin likitanci, kuma da haka kamfanin ya taimakawa marasa lafiya da dalar Amurka miliyin 10 zuwa 15 a ko wace shekara, idan da zasu yi aikin tiyatar a wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan ci gaban da aka samu zai rage lokacin da ake bukatar sanyawa marasa lafiya anesthesia na kashe zafi har’ ila yau ya rage lokacin da ake bukata na aikin tiyata daga awa guda zuwa minti 20 kacal.

Banda haka  ga kuma saukin kudin da za’a kashe idan an kwatanta da zuwa kasashen waje don samun irin wannan kayakin aiki, ko kuma amfani da na’urar, amma wacce aka shigo da ita daga kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments