Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da muhawarar da ‘yan takarar neman shugabancin kasar Iran suke yi a gidan talbijin, gabanin zaben da za a gudanar a ranar 28 ga watan Yuni, yana mai cewa suna baiwa mutane masaniya kan ra’ayoyi da kuma shirye-shiryen da ‘yan takarar shida suke da su idan sun samu nasara.
Jagoran ya bayyana hakan ne a safiyar yau Asabar a wata ganawa da jami’an shari’ar kasar, bayan da ‘yan kasar suka kalli kashi uku cikin biyar na muhawarar da aka shirya kwanaki kafin kada kuri’ar maye gurbin shugaba Ihrahim Raeisi, wanda ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.
Sai dai Ayatullah Khamenei ya gargadi ‘yan takarar da su guji furta kalamai da ka iya farantawa makiya Iran rai.
“Shawarata ita ce, wannan tattaunawa da ‘yan takarar ke yi tare da juna a gidajen talabijin, ko kuma maganganun da suke yi ko dai a bainar jama’a ko kuma daidaikunsu domin a samu nasara a kan abokin hamayya, kada su kunshi wani abu da zai faranta ran makiyanmu,” in ji Jagoran.
“Bai kamata kalaman da ake furtawa su faranta wa makiyan kasa rai ba, wannan bai halatta ba,” inji shi.
“Abin da ake zato shi ne cewa dukkan ‘yan takara suna son Iran da Jamhuriyar Musulunci, da kuma yi wa al’umma hidima, don haka bai kamata su rika yin magana da za ta faranta wa makiya rai ba.”
A muhawararsu ta uku, ‘yan takarar sun gabatar da tsare-tsarensu kan al’amuran al’adu da zamantakewar kasar, wanda kuma wannan ya biyo bayan taron muhawara na farko da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata, da kuma mataki na biyu a ranar Alhamis, wanda ya shafi tattalin arziki da zamantakewar al’umma.