Limamin da ya jagorancin sallar Jumma’a a nan Tehran Aya. Ahmad Khatami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun sha alwashin daukar fansar jinin shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya wanda ma’aikatan HKI suka kashe a nan tehra.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto limamin yana fadar haka a cikin hudubobinsa na sallara Jumma’a a yau a nan birnin Tehran.
Aya. Khatami ya kara da cewa HKI da kuma Amurka suna tarayyar a ta’asan da take aikatawa a zirin Gaza, haka ma a kissan shugaban kungiyar Hamas a nan Tehran Amurka tana da hannu cikin sa.
Limamin ya nakalto Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Aya. Sayyid Aliyul Khaminae yana fada dangane da kissan Haniya kan cewa: Wajibin JMI ta dauki fansar kissan Haniyya.
Limamin ya kara da cewa lokaci da kuma ta wurinda za’a dauki fansar sai bayan an dauki fansar ne kawai kowa zai gane.
Banda haka Aya. Khatami ya kara da cewa, zaben Yahya Sinwar a matsayin wanda zai maye gurbin Isma’ila Haniyya a shugabancin kungiyar Hamas zabi ne wanda ya dace, kuma wata duka ce mai karfi kan HKI.
Saboda Sinwar yana da tarihi mai kyau na gwagwarmaya da HKI, daga cikin ya zauna gidan kaso na tsawon shekaru 20. Sannan ya taba fadawa yahudawan kan cewa lokaci na zuwa da zaku shiga hannummu.