Iran: Harin Isra’ila kan asibitin a iyakar Lebanon da Siriya laifin ne

Iran ta yi kakkausar suka kan harin da Isra’ila ta kai kan wani asibitin agaji da ke kan iyakar Syria da Lebanon, inda ta bayyana

Iran ta yi kakkausar suka kan harin da Isra’ila ta kai kan wani asibitin agaji da ke kan iyakar Syria da Lebanon, inda ta bayyana shi “laifi ne na yaki.”

“Harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a asibitin kungiyar agaji ta Red Crescent ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Siriya, tare da ma’ajiyar magunguna a ranar 9 ga watan Oktoban 2024, tare da haifar da gobara a wurin, da kawo cikas mai tsanani wajen gudanar da ayyukan jin kai, wannnan yana a matsayin laifin yaki,” in ji Kazem Gharibabadi, mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin shari’a da harkokin kasa da kasa.

Ya kara da cewa cin zarafi da Isra’ila ke yi da keta ka’idoji da dokokin jin kai na kasa da kasa kamar yadda aka tsara a cikin yarjejeniyoyin Geneva guda hudu na 1949 da ka’idojin jin kai na kasa da kasa, wanda suka haramta duk wani hari a wuraren fararen hula, musamman wuraren kiwon lafiya da asibitoci, yin hakan laifin yaki.

Harin na Isra’ila ya yi sanadin lalata motocin daukar marasa lafiya da dukkan kayan aikin jinya da ke cikin cibiyar, wadda aka kafa domin taimakawa ‘yan Lebanon da suka rasa matsugunansu a kan iyakar Syria da Lebanon.

Asibitin ya kuma kunshi kayyakin abinci, da na’urorin kiwon lafiya, da magunguna, wadanda dukkansu ke dauke da tuta da alamomin kungiyar agaji ta Red Crescent.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments