Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce babu daya daga cikin laifukan da Isra’ila ta aikata da ba za ta fuskanci sakamako a kansa ba.
Nasser Kan’ani ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na mako-mako da ake yi a birnin Tehran a wannan Litinin, yayin da aka tambaye shi dangane da matakin da Iran za ta dauka dangane da kisan da aka yi wa Sayyed Hassan Nasrallah, ta hanyar gagarumin hari da jiragen yakin na Isra’ila, da aka yi amfani da bama-bamai na bunker-buster da Amurka ta baiwa Isra’ila.
Sai ya amsa da cewa: “Iran za ta ci gaba da kokarinta na siyasa da doka, kuma za ta aiwatar da mataka da kuma hukuncin day a dace da hakan.”
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin karfin da kasashen musulmi suke da shi wajen hukunta Isra’ila, ya kara da cewa: al’ummar Palastinu na da hakki a kan kasashen musulmi da su yi amfani da karfinsu wajen yin matsin lamba a kan gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Ya zuwa yanzu dai Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gaza fitar da wani kudiri na hana gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata laifuka yaki, saboda rawar da Amurka take takawa game da hakan.