Iran da China sun tattauna batun inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani ya bayyana a ranar Asabar din nan cewa, gwamnatocin kasashen Iran da China sun kudiri aniyar

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani ya bayyana a ranar Asabar din nan cewa, gwamnatocin kasashen Iran da China sun kudiri aniyar kara inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Wannan bayanin ya biyo bayan ganawarsa da jakadan kasar Sin a Tehran Zong Peiwu, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ayyukan hadin gwiwa tsakanin Tehran da Beijing.

Bagheri Kani ya bayyana cewa, Iran da Sin suna taka muhimmiyar rawa a matakai na kasa da kasa, kuma kasancewarsu mambobi a kungiyoyi daban-daban da hakan ya hada da BRICS.

Ambasada Zong Peiwu ya yi na’am da wannan ra’ayi, inda ya bayyana cewa, amincewa da juna a siyasance da kuma azamar da jami’an kasashen biyu suka yi, sun kafa tushe mai tushe na hadin gwiwa tsakanin Tehran da Beijing.

Ya kuma tabbatar da aniyar kasar Sin na aiwatar da cikakken shirinta na hadin gwiwa tare da Jamhuriyar Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments