Amir-Hossein Ghazizadeh Hashemi daya daga cikin ‘yan takara shida da ke neman zama shugaban kasar Iran ya fice daga takarar.
Hashemi, wanda tsohon dan majalisa ne kuma mataimakin shugaban kasa, ya bayyana janyewarsa daga takarar a wata sanarwa a ranar Laraba.
Ya bayyana dalilin shigarsa takarar a matsayin kare tafarkin tsohon shugaban kasar Ebrahim Raeisi, wanda ya yi shahada a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayu tare da mukarabansa, lamarin da ya sa kasar ta tsara gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Yuni.
A cikin bayanin nasa, Hashemi ya ce ya yi alfahari da samun damar yin aiki tare da Raeisi.
Ya bayyana cewa bai yi “kokari ba” don kare muradun tsohon tsohon shugaban kasar a lokacin da yake yakin neman zabe ba.
Tunda farko dai da yake halartar wani taron siyasa da aka watsa a ranar Laraba, dan takarar wanda a halin yanzu yake shugabantar gidauniyar shahidai da tsoffin soji, ya yi alkawarin daukar kwararan matakai na diflomasiyya.
Ya kuma sha alwashin ci gaba da dabarun huldar kasa da kasa na shugaban kasar mirigayi Ra’isi wanda ya samar da nasarori da dama.
‘Yan takaran da suka rage a zaben na gobe sun hada da Saeed Jalili tsohon shugabana tawagar tattaunawa kan batun nukiliyar kasar, da Mohammad Baqer Qalibaf, kakakin majalisar dokokin Iran, da Mostafa Pourmohammadi, tsohon ministan cikin gida, Masoud Pezeshkian, tsohon ministan lafiya, da Alireza Zakani magajin garin Tehran.