Iran: Al Sisi ya taya Pezeshkian murnar lashe zaben shugaban kasa

Gwamnatin kasar Masar ta taya Masoud Pezeshkian murnar lashe zaben da aka yi masa a matsayin sabon shugaban kasar Iran. A cewar sanarwar da mai

Gwamnatin kasar Masar ta taya Masoud Pezeshkian murnar lashe zaben da aka yi masa a matsayin sabon shugaban kasar Iran.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Masar Ahmed Fahmy ya fitar, shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban kasar Iran Pezeshkian, yana mai cewa nasarar da ya samu na nuni da irin kwarin gwiwar da al’ummar Iran suke da shi a kansa na iya yin hidima ga kasarsa da kuma yin aiki tukuru wanda zai kai shi zuwa ga ci gaban kasarsa.

Al Sisi ya kuma yi wa sabon shugaban fatan samun nasara a ayyukansa tare da nuna jin dadinsa ga kyakkyawar alakar da ke tsakanin al’ummar Masar da Iran.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana son yin hadin gwiwa da Pezeshkian, kamar yadda mai magana da yawun babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyana, ya ce majalisar  tana son yin hadin gwiwa da sabon shugaban kasar Iran.

“Muna fatan yin aiki tare da sabon shugaban na Iran,” in ji shi a wani taron manema labarai.

Pezeshkian, mai shekaru 69, wanda kuma kwararren likitan zuciya ne kuma dan majalisa, ya lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu na ranar Juma’a inda ya samu kuri’u miliyan 16.3, yayin da abokin hamayyarsa Saeed Jalili ya tashi uri’u miliyan 13.5.

A cikin jawabinsa, Pezeshkian ya bayyana nasararsa a matsayin farkon “sabon babi” ga kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments