Iraki Ba Ta Amince Da Keta Samaniyarta Ba Domin Kai Wa Makwabtanta Hari

Babban mai bai wa gwamnatin Iraki shawara akan harkokin tsaro Kasim al-aaraji ya bayyana a yau Lahadi cewa; Kasar Iraki tana yin duk abinda za

Babban mai bai wa gwamnatin Iraki shawara akan harkokin tsaro Kasim al-aaraji ya bayyana a yau Lahadi cewa; Kasar Iraki tana yin duk abinda za ta iya cikin karfinta domin ganin ta hana afkuwar yaki a cikin wannan yankin.

Al-aaraji  ya kuma kara da cewa, kasar tasa tana aiki da dukkanin kungiyoyin kasa da kasa domin ganin an kawo karshen mummunan yanayin da ake ciki a Gaza da kuma Lebanon.

Babban jami’in tsaron na kasar Iraki ya kuma ce a yayin ziyarar da ya kawo zuwa Iran ya tattauna da jami’an gwamnatin kasar, inda ya tabbatar musu da cewa, Iraki ba ta son ganin kowane bangare ya yi amfani da sararin samaniyarta domin kai wa makwabtanta hari.

Iraki dai kasa ce da take a yammmacin Asiya wacce kuma take makwabtaka da Iran, sannan kuma ta yi tarayya da ita a cikin addini, da al’adu da kuma manufofi na siyasa. Haka nan kuma kasashen biyu suna cikin masu kare ‘yan gwgawarmaya da taimaka musu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments