Hukumar IAEA Ta Fara Taronta Na Wannan Fasali A Yau Litinin A Birnin Vienna

Gwamnonin hukuma mai kula da al-amuran makamashin Nukliya ta kasa da kasa ta fara taronta na kwanaki biyar a birnin Vienna, inda ake saran gwamnonin

Gwamnonin hukuma mai kula da al-amuran makamashin Nukliya ta kasa da kasa ta fara taronta na kwanaki biyar a birnin Vienna, inda ake saran gwamnonin zasu tattauna al-amura da dama.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar hukumar na cewa agendar taron gwamnonin hukumar ta IAEA sun hada da samar da aminci dangane da sarrafa makamashin Nukliya a duniya, karfafa ayyukan hukumar don samun ci gaba a ayyukan sarrafa makamashin nukliya a duniya, bincike da kuma tabbatar da irin ayyukan da JMI ta ke yi dangane da shirinta na makamashin nukliya karkashin kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231 ta (2015).

Har’ila yau a cikin agendar taron na gwamnonin IAEA akwai bukatar kasar Korea ta kudu dangane da tsaro da lafiyar makamashin nukliya, karfafa yarjeniyar NPT a yankin gabas ta tsakiya da sauransu.

Ana saran shugaban hukumar ta IAEA Rafael Grossi zai yi jawabi ga kafafen yada labarai don karin bayani kan ayyukan taron na kwanaki 5 masu zuwa.

Banda haka idan an kammala taron ana saran shugaban hukumar har’ila yau zai sake zantawa da yan jarida don sanin inda aka kwana kan wadannan al-amura.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments