Houthi : Zamu Ci Gaba Da Kai Hare-hare Isra’ila Har Sai An Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza

Jagoran kungiyar Ansarullah da aka fisani da ta ‘yan Houthi a Yemen, ya sake jaddada goyon bayan kasar ga Falasdinawa wadanda ke fuskantar yakin kisan

Jagoran kungiyar Ansarullah da aka fisani da ta ‘yan Houthi a Yemen, ya sake jaddada goyon bayan kasar ga Falasdinawa wadanda ke fuskantar yakin kisan kiyashin Isra’ila.

Abdul-Malik al-Houthi ya bayyana hakan ne a bikin da aka gudanar a ranar Lahadin na Maulidin Annabi Muhammad (SAW) a birnin Sana’a inda dubban ‘yan kasar Yemen suka taru.

Ya ce harin makami mai linzami na baya-bayan nan da Yemen ta kai, wani bangare ne na ci gaba da kai hari kan Isra’ila.

Houthi ya jaddada cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan kyamar Isra’ila har sai gwamnatin ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi a zirin Gaza da kuma killace yankin.

Zamu ci gaba da tsaya tsayin daka har sai an tsarkake Falasdinu daga kangin mamayar,” inji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments