HKI Tana Shishigi Cikin Zaben Shugaban Kasar Amurka Na Watan Nuwamba Mai Kamawa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ila Baghae yace yahudawan Sahyoniyya ne suke shishigi a cikin zabubbukan shugaban kasa wanda za’a gudanar a ranar 5

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ila Baghae yace yahudawan Sahyoniyya ne suke shishigi a cikin zabubbukan shugaban kasa wanda za’a gudanar a ranar 5 ga watan Nuwamba mai kamawa a kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakato Baghae yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa HKI tana son jawo dukkan kasashen yankin Asiya ta kudu shiga yakin da take yi a gaza da Lebanon don cimma wasu manufofinta a zaben shugaban kasar Amurka a cikin watan nuwamba mai zuwa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa, a dai dai wannan lokacin ne gwamnatin kasar Amurka take zargin kasar Iran da shishigi cikin zaben shugaban kasar ta Amurka. Bayan ta san wanda ke shishigi a cikin zaben a ciki da wajen kasar ta  Amurka.

Ya kara da cewa jam’iyyar Democrate ta shugaban Biden tana kokarin sake lashe zaben shugaban kasa karo na biyu, don haka tana neman duk wani abu da zai jawo hankalin Amurkawa masu zabe su zabi jam’iyyar.

Shugaba biden dan shekara 81 a duniya, ya janye daga takarar shugabancin kasar a ranar 21 ga watan yulin da ya gabata bayan ya sha kaye a muhawararsa da Donala Trump, sannan yan jam’iyyarsa suka tilasyawa janyewa daga takarar. A nan ne sai ya mikawa mataimakiyarsa Kamala Haris, amma yakin da ke faruwa a gaza yana iya zama masu matsala a samun kuri’un masu zabe a zaben na ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa. Bayan zaben dai a cikin watan Janerun shekara ta 2025 ne shugaban da ya lace zaben zai karbi shugabancin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments