Isra’ila Ta Yi Wa Shugaban Kasar Turkiya Barazanar Kisa

Ministan harkokin waje na HKI “Yisrail Kats” ya wallafa hoton shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan a shafin “X” sannan ya kuma rubuta cewa: Yana

Ministan harkokin waje na HKI “Yisrail Kats” ya wallafa hoton shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan a shafin “X” sannan ya kuma rubuta cewa: Yana yi wa Isra’ila baraza, don haka mutuwa ce a gabansa.”

Shi dai shugaban kasar Turkiya yana Magana ne akan abubuwan da suke faruwa a Falasdinu, inda ya bayyana cewa; Wajibi ne kasar Turkiya ta zama mai karfi, saboda kada Isra’ila ta yi abinda take yi a Falasdinu.

Bugu da kari shugaban kasar ta Turkiya ya bayyana cewa; Turkiya za ta iya  shiga cikin Isra’ila, kamar yadda ta shiga Libya da kuma yankin “Qareh-Bah’ na Azerbaijan.”

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Turkiya ta fitar da bayanin mayar da martani da aciki ta bayyana cewa;  Wadanda su ke yi wa Falasdinawa kisan kiyashi su kwana da sanin cewa ba su isa su kawo karshensu ba.

Sanarwar ta kuma kara da cewa; Kamar yadda kisan kiyashin Hitler ya zo karshe, to kiashin kiyashin na Benjamine Netenyahu yake yi, shi ma zai zo karshe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments