HKI Ta Yi Sabbin  Kisan Kiyashi Uku A Falasdinu

Mutane 17 ne su ka yi shahada a yau Juma’a a Gaza sanadiyyar hare-hare da jiragen yaki da HKI ta kai a sassa daban-daban. Ma’aikatar

Mutane 17 ne su ka yi shahada a yau Juma’a a Gaza sanadiyyar hare-hare da jiragen yaki da HKI ta kai a sassa daban-daban.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta bayyana cewa, a daidai lokacin da hare-haren HKI suke cika kwanaki 364, sojojin mamayar sun yi kisan kiyashi har sau uku a cikin sa’o’i 24.

Sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta ce; an kai gawawwakin shahidai 14 zuwa asibitocin yankin bayan da baya aka riga aka kai wasu shahidan 50.

Bugu da kari ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinu ta kuma ce, da akwai gawawwakin wasu shahidai a karkashin baraguzai, da kuma kan hanyoyi da ba a kai da dauko su zuwa asibitoci ba.

Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada a cikin shekara daya sun kai 41,802, yayin da adadin wadanda su ka jikkata su kai 96,844.

A wani labarin kuwa, acan garin Khan Yunus, an fito da gawawwanin kananan yara biyu da su ne Majid Muntasar da kuma Ahmad Salih al-Fara, bayan da sojojin HKI su ka kai wa gidansu hari kwanaki biyu da su ka gabata.

A beit Lahiya ma sojojin HKI sun kai hari da jirgi maras matuki da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa biyu. A rewacin yankin Gaza, a gabar ruwa wan Bafalasdine daya ya yi shahada saboda harin da kananan jiragen ruwan HKI su ka kai wa yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments