HKI Ta Sanya Ayatullah Sistani Cikin Jerin Wadanda Take Son Yi Wa Kisan Gilla

Tashar Talbijin din HKI ta “Channel 14” ta watsa hotunan wasu fitattun ‘yan gwgawarmaya da HKI take son kashewa da su ka hada Yahya Sinwar

Tashar Talbijin din HKI ta “Channel 14” ta watsa hotunan wasu fitattun ‘yan gwgawarmaya da HKI take son kashewa da su ka hada Yahya Sinwar na Hamas, kwamandan rundunar Kudus ta IRGC, Isma’ila Qa’ani, jagoran juyin musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei, Abdulmalik al-Husi na Yemen, sai kuma Ayatullah Sistani babban marjam’in shi’a na duniya dake Iraki.

Tare da cewa, tashar talabijin ta HKI ba ta amabci dalilin sanya sunan Ayatullah Sistani a cikin jerin wadanda ake son kashewa ba, sai dai a filin yake cewa, yana cikin wadanda su ka fara yin kira da a taimakawa Falasdinawa a yakin da HKI ta shelanta akansu tun shekarar da ta gabata. Bugu da kari Ayatullah Ali Sistani ya yi kira da a kawo karshen yakin da ‘yan sahayoniyar suka shelanta akan al’ummar Lebanon a cikin makwanni kadan da su ka gabata.

Shugaban kungiyar malaman addinin musulunci na kasar Iraki Sheikh Khalin Mullah ya zargi HKI da kokarin shelanta yakin addini.

Sheikh Khalid Mullah ya kuma ce saboda yadda Isra’ila take shan kashi ne, ta ke kokarin bude yakin addini a wannan lokacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments