Hezbullah ta kaddamar da hare-hare da manyan makamai masu linzami a kan Tel Aviv

Majiyoyin sojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa, Hizbullah ta harba wasu manyan makamai masu linzami a kan birnin Tel Aviv a jiya Litinin,

Majiyoyin sojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa, Hizbullah ta harba wasu manyan makamai masu linzami a kan birnin Tel Aviv a jiya Litinin, lamarin da ya haifar da babbar barna da kuma katsewar wutar lantarki a sassan yankin.

An bayyana cewa, mutane da dama sun jikkata, sannan akalla biyu suka halaka, amma  yanzu gwamnatin yahudawan ba ta bayyana adadin na karshe ba.

Wata kafar yada labaran Isra’ila ta rawaito cewa makamin da aka harba daga kasar Labanon da ya sauka a Tel Aviv makami mai linzami ne samfurin Fateh 110.

Wannan makami mai linzami yana  karfi wajen haifar da barna mai yawa a duk inda ya sauka, kuma wannan shi ne karon farko da kungiyar Hizbullah ta fara harba wanann makami, wanda zai kawo daidaito a yakin da ake yi a yankin.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito cewa daya daga cikin makaman ya sauka a Ramat Gan da ke tsakiyar birnin Tel Aviv, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a yankin baki daya.

Baya ga haka kuma Wata gobara ta tashi a yankin gabashin birnin Tel Aviv, bayan da wani makami mai linzami da Hizbullah ta harba a sauka a yankin a wani sansani na sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments