Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kaddamar da wasu munanan hare-hare na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke kai wa kan kasar Labanon, tare da jaddada goyon bayanta ga Falasdinawa a Gaza.
Harin farko da aka kaddamar a ranar jiya litinin, an ga mayakan Hezbollah sun harba makaman roka samfurin Grad a sansanin sojin Isra’ila dake kudu maso yammacin Kiryat Shmona. Harin makamin roka dai ya zo ne a matsayin martani ga harin da Isra’ila ta kai kan Chaqra da ke Kudancin Lebanon.
Daga baya a yammacin ranar litinin, dakarun Hizbullah sun kaddamar da hare-hare biyu, na farko sun kai hari ne a wani wuri na sojojin mamaya na Isra’ila a sansanin al-Raheb.
Mayakan na Hizbullah sun yi amfani da makami mai linzami mai sarrafa kansa wajen ragargaza tankokin yakin yaki.
Mintuna biyar bayan haka, Hizbullah ta harba makamai da ba a tantance ba a sansanin sojin Isra’ila na al-Malikiyya, inda suka nufi wata na’urar leken asiri da Isra’ila ta girka a wurina a cikin ‘yan kwanakin nan, inda ta ragargaza wurin baki daya.
Har ila yau mayakan na Hizbullah sun lalata na’urorin da aka kafa a baya-bayan nan a tsaunin al-Karantina, inda suka tarwatsa su gaba daya.
Hakan nan kuma mayakan Hezbollah sun kuma yi wa tankokin yaki na Merkava na Isra’ila kwanton bauna a ranar Litinin, bayan da suka sanya ido kan motsin sojojin Isra’ila a sansanin sojin na al-Raheb, inda suka samu nasarar ragargaza wasu daga cikin tankokin yakin na sojin Isra’ila ta hanyar harba makaman ATGM a kansu.