Da sanyin safiyar wannan Asabar ne kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon Hezbollah, ta kaddamar da wasu hare-hare da makamai masu linzami a kan wasu muhimman wurare na sojin Isra’ila a Haifa, yayin da kuma a daya bangaren mayakan kungiayr ke ci gaba da dakile yunkurin sojojin Isra’ila na kutsawa cikin kasar Lebanon ta kan iyakan kasar.
Kungiyar Hizbullah ta tabbatar da cewa, ayyukanta sun zo ne domin kare kasar Labanon, da ikonta, da al’ummarta, da kuma goyon bayan Gaza da kuma tsayin daka mai daraja.
Farmakin na 12 ga Oktoba 2024, ya fara ne tun da jijjifin safiya har zuwa karfe 1 na rana.
A daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin kungiyar Hizbullah da jami’an sojin haramtacciyar kasar Isra’ila, Hizbullah na kara zafafa hare-harenta akan muhimamn wurare na sojin musamman rumbunan makamai da kuma wuraren kera su.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a dakin gudanar da ayyukanta a kasar Labanon ta bayyana cewa, makamai masu linzami da jiragen yakin marasa matuka na kungiyar Hizbullah na ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin soji da matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna a cikin yankunan falastinawa da suka mamaye arewacin Falastinu.