Harin Jirgi Maras Matuki Daga Iraki Ya Yi Sanadiyyar Kashe Sojojin HKI Biyu A Yau Juma’a

 A yau Juma’a ne majiyar sojan HKI ta sanar da cewa sojojinta biyu sun mutu sanadiyyar jirgi maras matuki da aka harbo daga Iraki, ya

 A yau Juma’a ne majiyar sojan HKI ta sanar da cewa sojojinta biyu sun mutu sanadiyyar jirgi maras matuki da aka harbo daga Iraki, ya kuma fada akan sansanin soja dake tuddan Gulan dake karkashin mamaya.

Tun a jiya Alhamis ne dai majiyar  ‘yan gwagwarmayar Iraki  su ka nasar da kai hare-hare har sau uku da jirage marasa matuki zuwa yankin kudancin Falasdinu dake karkashin mamaya.

Sanarwar ‘yan gwgawarmayar na Iraki ta kunshi cewa,matukar HKI ta cigaba da kai wa Gaza hari, to kuwa za ta fuskanci hare-hare masu tsanani.

Dama dai tun farkon yakin Gaza ne da yake cika shekara daya, ‘yan gwgawarmayar na Iraki su ka shiga cikin sahun masu kai wa HKI da ma Amurka hare-hare da zummar taimakawa Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments