Majiyoyin Tsaro a Najeriya sun rawaito cewa: Mutane akalla 18 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kai cikin taron daurin aure a garin Gwoza da ke jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin kasar.
Harin kunar bakin wake na farko da aka kai ya lashe rayukan mutane shida ne a wurin wani bikin aure, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Asabar. Sannan harin kunar bakin waken na biyu wata ‘yar ina ga kisa ce dauke da wani yaro a bayanta ta tayar da bama-bamai a cikin jama’a da suka halarci bikin daurin aure a garin Gwoza, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Nahum Kenneth Dasu ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa.
A nashi bangaren Barkindo Sa’idu, shugaban masu aikin ceto na yankin da ke garin Gwoza ya ce: Da misalin karfe 3 na rana, bam na farko ya tashi a Gwoza, wanda wata ‘yar kunar bakin wake ta tayar a wajen wani bikin aure.
Rahotonni sun tabbatar da mutuwan mutane 18 a hare-haren, da suka hada da yara, maza, mata da mata masu juna biyu, yayin aka samu wadanda suka samu raunuka da yawansu ya kai 19 da aka dauke su cikin motocin daukar marasa lafiya hudu zuwa babban birnin yankin, Maiduguri.