Hare-haren Isra’ila Sun Yi Ajalin Falasdinawa 53 A Gaza Da Kuma 21 A Lebanon

Sojojin Isra’ila sun kashe akalla mutane 53 a Gaza da kuma wasu 21 a Lebanon a ranar Lahadi, yayin da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Sojojin Isra’ila sun kashe akalla mutane 53 a Gaza da kuma wasu 21 a Lebanon a ranar Lahadi, yayin da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana kaduwarsa kan “mummunan yanayin da ake ciki.

Hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a kudancin kasar Lebanon, a cewar ma’aikatar lafiya ta Lebanon.

Akalla mutane 9 ne suka mutu sannan wasu 38 suka jikkata a wani harin da aka kai kan Haret Saida, kusa da birnin Sidon mai tashar jiragen ruwa, in ji ma’aikatar a ranar Lahadi.

Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ba da rahoton mutuwar mutane 2,464 a kasar, yayin da a kalla 11,530 suka jikkata tun daga watan Oktoban 2023.

A Falasdinu kuwa akalla Falasdinawa 42,924, akasarinsu fararen hula aka kashe a zirin Gaza, a cewar ma’aikatar lafiya ta gwamnatin Hamas.

A halin da ake ciki dai an ci gaba da sabuwar tattaunawa a wannan Lahadin a birnin Doha tsakanin Isra’ila da Amurka da kuma  Qatar domin tattauna tsagaita wuta a Gaza da nufin sako Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments