Babban kusa a kungiyar Hamas Osama Hamdan ya tabbatar da cewa tattaunawar baya-bayan nan tsakanin Hamas da Fatah a Masar dangane da gudanar da lamurran Gaza ta kasance mai inganci da armashi.
Wannan bayani ya zo daidai da abin da wata majiyar Falasdinawa ta bayyana wa tashar talabijin ta Al Mayadeen, inda ta bayyana taron na ranar Lahadi kan gudanarwa da hada kai a kan lamarin Gaza a matsayin mai fa’ida matuka.
Da yake magana a wani taron manema labarai, Hamdan ya bayyana cewa, tattaunawar ta tabo batutuwan da suka shafi kasar Falasdinu, tare da mai da hankali kan hare-haren da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a zirin Gaza da kuma dabarun dakile shirin mamaye yankin.
Bangarorin biyu sun kuma tattauna batun kafa wani kwamitin hadin gwiwa da zai kula da bukatun yankin Gaza, inda suka jaddada cewa, kula da harkokin Falasdinu a Gaza, da gabar yammacin kogin Jordan, da sauran yankunan Falastinu, ya kamata ya zama wani lamari na Falasdinu kadai, wanda kuma hakan batu ne da aka cimma shi a matsayin kudiri na kasa da kasa.
Hamdan ya yi nuni da cewa, za a ci gaba da tattaunawa tsakanin Hamas, Fatah, da sauran bangarorin Palasdinawa a kokarin cimma matsaya da za ta tallafa wa al’ummar Palasdinu, musamman a Gaza.
Ya kuma bayyana cewa, Hamas na yin cudanya da sauran bangarori na yankin da na kasa da kasa, domin hada kai don kawo karshen hare-haren da ake kai wa Gaza. “Wannan yunkuri a bude yake ga shawarwarin da za su tabbatar da tsagaita bude wuta da kuma janye sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila daga yankin Gaza,” in ji shi.