Hamas ta yi Allah wadai da azabtar da Falasdinawa a gidan kason Isra’ila

Hamas ta yi Allah wadai da azabtar da Falasdinawa shida waɗanda suka hada da mata biyu da aka sako daga gidajen yarin Isra’ila. A wata

Hamas ta yi Allah wadai da azabtar da Falasdinawa shida waɗanda suka hada da mata biyu da aka sako daga gidajen yarin Isra’ila.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu ta bayar da misali da shaidar da ta samu daga wurin fursunonin da aka sako wadda kamfanin dillancin Labarai na Anadolu ya tattaro.

Falasdinawa sun bayyana cewa sun fuskanci “mummunar azabtarwa da duka a tsawon lokacin da suke tsare.”

Hamas ta ce azabtarwar da aka yi musu “tana nuna yanayin da dubban fursunoni da sauran Falasɗinawan da aka tsare suke fuskanta a mamayar Isra’ila da kuma hukunci a cibiyoyin tsarewa irin salon ‘yan Nazi.”

Kazalika kungiyar ta jaddada cewa irin wannan azabtarwa, ”waɗanda ba su da imani da tausayi da sanin ƙima da darajar ɗan’adam ne suke aiwatar wa a kan mutane masu rauni da ba su ji ba ba su gani ba.”

Ta ce fursunonin da aka sako “sun nuna alamun rashin lafiya saboda azaba da sakaci da yunwa da zagi da kuma rashin barci da suka fuskanta,” tana mai kira kan a gaggauta daukar mataki mai tsauri don fallasa abubuwan da ke faruwa a gidajen yarin Isra’ila da kuma ceto dubban Falasdinawa da ake tsare da su a wannan wuri- da ake aiwatar da salon tsarewa irin na Nazi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments