Hamas ta sanar da shahadar shugabanta Yahya Sinwar

Kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas ta sanar da shahadar shugaban ofishinta na siyasa kuma kwamandan farmakin guguwar Al-Aqsa, Yahya Sinwar. A cikin wata sanarwa da

Kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas ta sanar da shahadar shugaban ofishinta na siyasa kuma kwamandan farmakin guguwar Al-Aqsa, Yahya Sinwar.

A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta nuna girmamawa ga Sinwar, inda ta bayyana shi a matsayin daya daga cikin mutane masu daraja da jajircewa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu  ga al’ummarsu don ‘yantar da Falasdinu, da kare wurare masu tsarki na al’ummar musulmi.

Bayanin ya ce Sinwar “Ya yi imani da Allah, kuma Allah ya gasgata alkwarin Allah, kuma Allah ya zabe shi a matsayin shahidi tare da ‘yan uwansa da suka gabace shi,” in ji sanarwar

Hamas ta yi jimamin Sinwar a matsayin shugaba  kuma fitaccen mai fafutukar neman ‘yanci, inda ta yi nuni da cewa ya samu shahada a lokacin da yake fafutuka, da tsayawa tsayin daka a fagen daga da kuma fuskantar sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Babban kusa a kungiyar Hamas Khalil al-Hayya ya tabbatar da cewa Sinwar ya tsaya tsayin daka a kan kare  Gaza da al’ummarta har zuwa numfashin sa na karshe.

Ya kuma bayyana yadda shugabancin  Sinwar ke kara rura wutar juriya da sadaukarwa a tafarkin neman ‘yanci da rayuwa cikin karama da daukaka, wanda rayuwarsa baki daya ta kare wajen gwagwarmaya da tsarewa a gidajen kason Isra’ila, amma har zuwa nunfashinsa na karshe bai taba ja da baya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments