Hamas Ta Mayar Da Martani Kan Kisan Da Isra’ila Ta Yi Wa Falastinawa ‘Yan Gudun Hijira A Rafah

Akalla mutane 40 ne suka yi shahada yayin da wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan tantunan ‘yan gudun

Akalla mutane 40 ne suka yi shahada yayin da wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan tantunan ‘yan gudun hijira a wani sansani da ke arewa maso yammacin Rafah a kudancin Zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga gidan talabijin na Falasdinu cewa, mutane 40 da suka hada da kananan yara da dama ne suka yi shahada yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan tantunan ‘yan gudun hijira a kusa da hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke arewa maso yammacin Rafah.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta sanar da cewa, harin bam din da Isra’ila ta kai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a wani wuri mai aminci da ke kusa da birnin Rafah.

A yayin da take jaddada cewa wannan yanki da Isra’ila ta ware a matsayin wani yanki na jin kai, kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce, ma’ikatanta sun kwashe shahidai masu yawa tare da wadanda suka samu munanan raunuka .

A yammacin jiya Lahadin kungiyar Hamas ta yi kira ga Palasdinawa da su tashi tsaye don nuna adawa da kisan kare dangi da sojojin Isra’ila suke a birnin Rafah.

Sanarwar ta kara da cewa, La’akari da mummunan kisan gillar da yahudawan sahyoniyawan suka yi a yammacin jiya, a tantunan ‘yan gudun hijira Falastinawa mata da kananan yara, muna son al’ummar yammacin gabar kogin Jordan na birnin Kudus da kuma sauran yankunan Falastinawa da yahudawa suka mamaye, da su fara boren intifada kan wannan mummunan aiki.

A yau ne kungiyar Al-Qassam Brigades, reshen soji na kungiyar Hamas ta sanar da cewa ta kai harin ramuwar gayya kan Tel Aviv da makami mai linzami a matsayin martani ga kisan kiyashin da yahudawan sahyoniya suka yi wa fararen hula a Rafa da sauran yankunan Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments