Hamas Ta Ce Tashar Talabijin Ta MBC Ta Dulmuya Kanta A Kisan Kiyashin Da HKI Take Yi A Gaza

Wani babban jami’i a kungiyar Hamas ya bayyana cewa abinda wasu kafafen yada labarai masu watsa shirye -shiryensu da harshen larabci suke yi ya sa

Wani babban jami’i a kungiyar Hamas ya bayyana cewa abinda wasu kafafen yada labarai masu watsa shirye -shiryensu da harshen larabci suke yi ya sa suna da hannu dumu dumu a cikin kisan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sami Abu Zahri daga daga cikin shuwagabannin Hamas yana fadar haka a birnin Beirut na kasar Lebanon.

Labarin ya kara da cewa tashar talabijin ta MBC ta kasar Saudiya wacce take da cibiya a birnin London na kasar Burani ta shirya rahoto na musamman kan kungiyar Hamas inda a cikinsa ta ke kirin shahid Yahaya Sinwar shugaban kungiyar wanda HKI ta kashe shi a fafatawa a da shi a garin Rafah na zirin gaza, a cikin kwanakin da suka gabata a matsayin  ‘dan ta’adda ne’.

Zuhri ya kara da cewa, da alamun wasu sun rufe idanunsa, basa ganin irin kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza ha ya kai ga suna kiran falasdinawa masu gwagwarmayan neman yencin kan kasarsu a matsayin ‘yan ta’adda’.

Gwamnatin kasar Iraki dai, bayan watsa wannan rahoton ta kwace lasisin kamfanin MBC a kasar Iraki kuma ta bukaci ta kawo karshen aikinta a kasar. Bagu da kari mutane a birnin Bagdaza sun yi wata zanga zanga wacce ta kai ga kona ofishin tashar MBC da ke birnin Bagdaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments