Gwamnatin Tarayya Ta Fara Rabon Tirelolin Shinkafa 740 A Fadin Nijeriya

A wani yunkuri na shawo kan matsalar karancin abinci, gwamnatin tarayya ta kaddamar da rabon shinkafa tirela 740 a fadin Nijeriya. Ministan yada labarai da

A wani yunkuri na shawo kan matsalar karancin abinci, gwamnatin tarayya ta kaddamar da rabon shinkafa tirela 740 a fadin Nijeriya.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.

Kowacce daga cikin Jihohi 36 na Tarayya da Babban Birnin Tarayya (FCT) za ta karbi tirela 20 na shinkafa, inda kowace tirela ke dauke da buhuna kusan 1,200 (25kg).

Wannan ya kai kusan buhunan shinkafa 24,000 a kowace jiha, wanda za a rabawa marasa galihu.

Ministan ya nemi Gwamnonin Jihohin da su yi tsari mai kyau ta yadda rabon zai isa ga masu tsantsar bukata

Wannan dai na zuwa ne bayan da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da wani rahoto da ya nuna hauhawar farashi ya ƙaru zuwa kashi 34.19 a watan Yuni.

NBS ta ce idan aka kwatanta da watanni baya, kayayyaki sun sake yin tashin gwauron zabi a Najeriya.

A gefe guda kuma ’yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan halin matsi da ake fama da shi, yayin da kuma matasa a ƙasar ke shirin tsunduma zanga-zanga a farkon wagan Agusta.

Sai dai batun shiga zanga-zangar ya haifar da cece-kuce da tada jijiyar wuyar tsakanin matasa da malamai a ƙasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments