Gwamnatin kasar Saudiya ta bada sanarwan cewa ba za ta amince ta samar da huldar jakadanci da HKI ba matukar ba’a kafa kasar Palasdinu mai zaman kanta sannan gabacin birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar ba.
Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudiya ya bayyana cewa Yerima mai jiran gadon sarauta kuma firai ministan kasar ta saudiya ne Muhammad bin Salman ya bayyana haka a taron majalisar gudanarwa ta kasar wato majalisar shoora.
Mohammad ya kara da cewa gwamnatin kasar tana aiki tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa don Falasdinawa sun sami kasarsu a matsayin yentacciyar kasa.
A wani bangare kuma gwamnatin kasar ta saudiya ta bayyana cewa tana kokarin ganin an kawo karshen yake yake a kasar Sudan.
Duk tare da yakin da HKI ta shiga a gaza kimani shekara guda da ta gabata, gwamnatin kasar Amurka tana matsawa sarakunan kasar Saudiya lamba don samar da huldar jakadanci da HKI.