Gwamnatin Iran Ta Jinjina Wa Sojojin Kasar Kan Dakile Hare-Haren Isra’ila

Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta jinjina wa dakarun tsaron saman kasar saboda irin matakan da suka dauka na kare wuraren soji

Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta jinjina wa dakarun tsaron saman kasar saboda irin matakan da suka dauka na kare wuraren soji daga hare-haren da Isra’ila ta kai a wannan Asabar, tana mai cewa matakin ya farfado da martabar al’ummar Iran.

Al’ummar Iran na alfahari da karfin tsaron kasarsu kuma sun gamsu da hakan, in ji Mohajerani a ranar Asabar.

Da take tsokaci a hukumance dangane da hare-haren da Isra’ila ke babatun cewa ta kaiwa Iran, kakakin ta ce an samu barna kadan ne kawai, tana mai kira ga jama’a da kada su kula da jita-jita da hotunan karya da “wasu kafafen yada labarai ke yadawa” da kuma bin diddigin labarai ta kafafen yada labarai masu Magana a hukumance.

Ta ce Iran na da karfi kuma irin wadannan munanan ayyukan ba za su iya haifar mata da matsala ba, ta kara da cewa a halin yanzu kasar na cikin yanayi na yau da kullum, komai yana tafiya ba tare da wani tsaiko ba, an ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen sama kamar yadda aka saba.

A safiyar wannan Asabar ne ofishin hulda da jama’a na rundunar tsaron sararin samaniyar kasar Iran ya fitar da sanarwa, inda ya sanar da cewa, an dakile hare-haren da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan cibiyoyin soji a birnin Tehran, da lardin Ilam da ke yammacin kasar, da kuma lardin Khuzestan da ke kudu maso yammacin kasar, tare da yin nasara a kan makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments