Iran ta yi allah wadai da kakkausan murya da harin da Isra’ila t akai kan sansanin Al-Mawasi dake kudancin Gaza.
Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya yi kakkausar suka kan harin na Isra’ila wanda shi ne misali na baya bayan nan na hare haren da Isra’ila ke kaiwa sansanonin ‘yan gudun hijira a Gaza.
Nasser Kan’ani, ya ce gwamnatin Tel Aviv ba ta mutunta dokokin kasa da kasa.
Sama da mutane 45 ne suka mutu a harin, yayin da akalla mutane 60 suka jikkata a sansanin na tantuna dake kusa da Khan Younes a kudancin Gaza.
Jami’in diflomasiyyar na Iran ya ce “wadanan hare-haren kan fararen hula, gwamnatin ‘yan ta’addar Isra’ila ta sake nuna cewa ba ta bin kowace doka da ka’ida.”
Ya yi nuni da irin ta’asar da Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinawa a Zirin Gaza da kuma fadada wuce gona da iri da gwamnatin kasar ke yi a yankin yammacin Asiya wanda barazana ne ga zaman lafiya da tsaro a duniya.
Isra’ila ta kaddamar da kazamin yakinta a zirin Gaza, inda ta kai hari kan asibitoci, gidaje, da wuraren ibada, bayan da kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa suka kaddamar da harin ba-zata, na ranar 7 ga watan Oktoban bara.
Akalla Falasdinawa 41,020 ne aka kashe, yawancinsu mata da kananan yara, yayin da wasu 94,925 suka jikkata.