Gaza: Gwagwarmayar Falasdinawa Tana Cigaba Da Kai Wa Sojojin Mamaya Hari

 Kungiyar gwgawarmayar Falasdinawa  ta Hamsa a Gaza suna cigaba da kai wa sojojin mamaya hare-hare,inda a bayan nan su ka harba makamai akan wani gida

 Kungiyar gwgawarmayar Falasdinawa  ta Hamsa a Gaza suna cigaba da kai wa sojojin mamaya hare-hare,inda a bayan nan su ka harba makamai akan wani gida da sojojin HKI suke ciki.

Bugu da kari ‘yan gwgawarmayar sun kai hari akan wata mota ta  sojojin mamaya kamar kuma yadda su ka harbo da jirgin sama maras matuki.

Wadannan hare-hare din suna faruwa ne a daidai lokacin da yakin Gaza, yake cika kwanaki 386.

Dakarun na “Kassam’ sun kuma kai hari da makamin  “Yasin 105” akan tankokin yaki biyu tare da tarwatsu.

Kakakin dakarun “Kassam”  ne ya bayyana cewa sun kai hari akan tankokin yakin ne a sansanin ‘yan hijira na Jabaliya.

Su ma mayakan rundunar “ Kata’ibul-Mujahidin” sun sanar da kai hare-hare akan sojojin HKI a sansanin Jabaliya ta hanyar amfani da nakiyoyi.

Dakarun “Sarayal-Quds” na kungiyar jihadul-Islami sun sanar da cewa, sun harbo jirgin sama maras matuki samfurin “Code Cabtar”.

Jirgin na leken asirin ne da HKI take aikewa a sararin samaniyar Gaza, domin tattara bayanai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments