Kafafen yada labarai na Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan sun bada labarin shahadar Falasdinawa 5, biyu daga cikinsu mata, a lokacinda wani jirgin yakin HKI wanda ake sarrafashi daga nesa, wato ‘Drons’ ya kai hare hare a kan garin Tulkaram a jiya Talata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, sojojin yahudawan sun yi ta harbin motocin jami’an agaji don kada su isar da wadanda suka ji rauni zuwa asbitoci don ceto rayukansu.
A dayen bangaren kuma falasdinawa masu gwagwarmaya sun tada nakiyoyi masu karfi kuma da dama kan motocin sojojin yahudawa wadanda suke kokarin kutsawa cikin yankun falasdiwa a sansanin yan gudun hijira na Tulkaram.
Wasu kafafen yada labaran sun bayyana cewa sojojin yahudawa da dama ne suka jikata, saboda tada nakiyoyin da dakarun falasdinwa suka yi a kan hanyoyinsu ta shiga yankunansu. A wani labarin kuma wani bafalasdine dan shekara 33 a duniya mai suna Jihad Mohammed Hussein Shalalda ya yi shahada sanadiyyar harbin da sojojin HKI suka yi masa a tukaram a jiya talata.