Falasdinawa dubu 40 ne suka gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Al-Aqsa mai albarka a yau
Dubban Falasdinawa ne suka gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Al-Aqsa mai albarka a yau, bisa la’akari da tsauraran matakan soji da mahukuntan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka dauka kan shiga masallacin.
Ma’aikatar Kula da kayayyakin Musulunci a birnin Qudus ta kiyasta cewa kimanin Falasdinawa dubu 40 ne suka gudanar da sallar Juma’a a cikin Masallacin Al-Aqsa.
Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun hana Falasdinawa shiga cikin Masallacin Al-Aqsa domin gudanar da sallar Juma’a musamman ta kofar Asba’d, tare da tsananta bincike da tantance sunayensu, baya ga kama wasu da dama daga cikinsu.
Sojojin mamayar sun ci gaba da sanya takunkumi mai tsauri kan shiga Masallacin Al-Aqsa, musamman a lokacin sallar Juma’a, tare da hana Falasdinawa masu yawa yin sallah a cikin Masallacin.
Hukumomin gwamnatin mamayar sun kuma hana dubban Falasdinawa daga yankunan Gabar yammacin kogin Jordan shiga cikin birnin Qudus domin gudanar da sallah a Masallacin Al-Aqsa, saboda sun gindaya musu sharudda musamman sai sun samu izini na musamman kafin ba su damar ketare shingayen binciken sojoji da ke kewaye da birnin mai alfarma.