Euro-Mediterranean: Dole Ne MDD Ta Ayyana Yunwa A Arewacin Gaza

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean ta ce dole ne kungiyoyin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya da abin ya shafa su ayyana

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean ta ce dole ne kungiyoyin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya da abin ya shafa su ayyana yunwa a arewacin zirin Gaza a hukumance saboda Isra’ila ta hana shigar da kayayyaki da agaji ga mazauna yankin arewacin Zirin sama da kwanaki 50.

A cikin wani rahoto da ta fitar kungiyar ta ce, amfani da yunwa a matsayin makami, daya ne daga kisan kare dangi da Isra’ila take ci gaba da yi a yankin, wanda ya hada da kashe-kashen jama’a da kuma tilasta gudun hijira.

Rahoton ya ce “Saboda killace yankin mai dubban Falasdinawa, da Isra’ila ta yi hakan ya jefa marasa lafiya da dama a asibitoci uku a arewacin zirin Gaza, cikin hadarin yunwa,” in ji rahoton.

Isra’ila ta toshe duk wani agajin jin kai zuwa arewacin Gaza tun ranar 25 ga Satumba, in ji ta.

Rahoton ya ce mutanen da ke Arewacin Gaza na shan luguden bama-bamai na da gangan, kuma ba su da abinci, ruwan sha da magunguna.

Ta kara da cewa, “Duk wanda ya yi yunkurin guduwa domin neman wadannan bukatu, jiragen Isra’ila ne suka kai masa hari a kashe shi.”

Kungiyar ta Euro-Med Monitor ta ce tawagarta ta tattara bayanai masu ban tsoro daga Falasdinawa da aka tilastawa barin arewacin zirin Gaza dangane da tsananin yunwa da karancin abinci a can.

Rahoton ya ce “Al’ummar duniya na da alhakin daukan matakan shari’a domin dakatar da yaduwar yunwa a zirin Gaza.”

Dole ne a matsa wa Isra’ila lamba don dawo da kiwon lafiya, ruwa, da ayyukan tsafta a zirin Gaza da kuma samar da lafiya, in ji kungiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments