Dubun Dubatar Mutanen Yemen Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Bayan Falasdinu Da Lebanon

A jiya juma’a ne dubun dubatar mutanen Yemen su ka yi gangamin nuna goyonsu ga al’ummar  Gaza da kuma Lebanon da suke fuskantar hare-haren HKI.

A jiya juma’a ne dubun dubatar mutanen Yemen su ka yi gangamin nuna goyonsu ga al’ummar  Gaza da kuma Lebanon da suke fuskantar hare-haren HKI.

An yi gangamin ne a garuruwan Sa’adah, Rimah, da Ma’arib da aka bai wa taken; “Muna Tare Da Mutanen Gaza Da Lebanon; Muna Kuma Gargadin Masu Girman Kai Na Duniya.”

Gangamin na jiya dai ya zo ne a matsayin amsa kiran jagoran kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Husi, da ya yi a shekaran jiya Alhamis, inda ya bukaci al’ummar kasar da su fito domin jaddada nuna goyon bayansu ga al’ummun  Falasdinu da Lebanon.

Kusan kowace juma’a mutanen Yemen suna yi gangamin nuna goyon bayansu ga al’ummar Gaza da Lebanon da suke fuskantar hare-haren sojojin mamayar HKI.

Bugu da kari, sojojin kasar Yemen suna cikin na sahun gaba da suke kai wa manufofin HKI hare-hare a Falasdinu dake karkashin mamaya. Sojojin na Yemen suna amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki wajen kai hare-haren musamman a yankin Iliat.

Akan tekun “Red Sea” sojojin na kasar Yemen sun hana jiragen ruwan HKI kai da komowa, haka nan masu kai kayayyakin haja zuwa tashar jirgin ruwa ta Iliat.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments