Donald Trump Yana Son Zama Zakara A Rikicin Yankin Gabas Ta Tsakiya

Dan takaran shugabancin Amurka Donald Trump yana Shirin ganin ya yi nasara a kan Joe Biden a rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta

Dan takaran shugabancin Amurka Donald Trump yana Shirin ganin ya yi nasara a kan Joe Biden a rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya

Jaridar ‘Ha’aretz’ ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta rawaito cewa: Dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump yana son a rubuta karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya da sunansa, domin karya alfaharin bankwana ga shugaba Joe Biden bayan ya bar fadar Mulkin White House.

Jaridar ta ce: “A zahiri, Trump yana son a rubuta karshen yakin da sunansa – idan ya ci zabe – musamman don magance rikicin fursunoni a Gaza.”

Jaridar Ha’aretz ta kwatanta shahararriyar kalmar Trump (Make America Great Again) da yakin neman zaben shugaban Amurka Ronald Reagan a shekara ta 1980, lokacin da zaben ya mamaye rikicin garkuwa da Amurkawa a kasar Iran.

Jaridar yahudawan ta yi nuni da cewa: Shugaban Amurka Jimmy Carter ya gwada komai tun daga matsin lamba na diflomasiyya zuwa wani yunƙurin ceto da bai yi nasara ba, kuma a ƙarshe, Amurka ta bi hanyar wata yarjejeniya mai tsada don a sake ‘yan kasarta, yayin da Reagan ya ɗauki kambun nasara, kuma aka saki Amurkawan da aka yi garkuwa da su a ranar bikin rantsar da shi, lura da cewa: Wannan ita ce wulakancin da Trump ke so ga Joe Biden a matsayin kyautar rabuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments