Donald Trump na kan gaba a zaben shugaban kasar Amurka

Dan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump na kan gaba a zaben shugaban kasar Amurka bisa ga sakamakon da ke fitowa daga jihohin daban-daban na kasar.

Dan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump na kan gaba a zaben shugaban kasar Amurka bisa ga sakamakon da ke fitowa daga jihohin daban-daban na kasar.

Bayanan sun nuna cewa Donald Trump ya da adadin kuri’un wakilai masu zabe  267 yayin da abokiyar takararsa ta jam’iyyar Demokrats Kamala Harris take da 224.

Kowane dan takara na bukatar samun adadin kuri’un wakilai masu zabe 270 ko fiye kafin ya lashe zaben shugaban kasar.

Kamala Harris ‘yar takarar Democrat da takwaranta na Republican Donald Trump suna fafatawa ne domin shiga Fadar White House, inda aka rufe rumfunan zabe ranar Talata sannan kuma ake ci gaba da dakon sakamakon zaben.

Sakamakon wucin gadi na zaben da aka tattara ya nuna cewa Trump yana kan gaba a mafi yawan jihohi, inda wasu jihohin ma akwai tazara mai nisa tsakaninsa da Harris.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments