Daruruwan Yahudawan Sahyoniyya Sun Kutsa Cikin Masallacin Al-Aksa Tare Da Kariyar Jami’an Tsaron Kasar

Daruruwan yahudawan Sahyoniyya sun kutsa cikin masallacin Alaksa mai tsarki tare da samun kariyar jami’an tsaron yahudawan. Har’ila yau tare da su harda ministan harkokin

Daruruwan yahudawan Sahyoniyya sun kutsa cikin masallacin Alaksa mai tsarki tare da samun kariyar jami’an tsaron yahudawan. Har’ila yau tare da su harda ministan harkokin cikin gida mai tsatsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kutsawar yahudawan cikin masallacin Alaksa ya tada hankalin falasdinawa wadanda suka yi kokarin hanasu kutsawa, amma jami’an tsaron HKI sun yi ta dukansu da kulake da kuma wasu makaman.

Labarin ya kara da cewa yahudawa kimani 1,600 ne wadanda aka rarrabasu har zuwa tawagogi 13 suka kutsa cikin masallacin, inji hukumar ‘Waqf’ mai kula da masallacin.

Wata kungiyar yahudawan Sahyoniyya wacce ake kira ‘Tisha BiAv’ ce ta bukaci a gudanar da bukukuwan na yau Talata a cikin masallacin Al-Aksa, don tunawa da musibun da suka fadawa yahudawa a tarihin su.

Hukumar ‘Wakf’ ta bayyana cewa jami’an tsaron yahudawan sun toshe dukkan kofofin shiga masallacin, sun kuma hana hatta bude shaguna a kasuwanni kusa da masallacin wanda ya kai ga tashe tashen hankula a wajen masallacin tare da wasu Falasdinawa.

Labarin ya kara da cewa yahudawa yan share wuri zauna sun shiga masallacin daga kofar Magariba, ta inda suka saba shiga idan zasu yi irin wannan keta hurumin. Sannan sun daga tutar yahudawan a mashiga ta kofar Al-Salasila ta masallacin na Al-Aksa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments