Danganta ‘Yan Jaridan Gaza Da ‘Yan Ta’adda Da Isra’ila Ke Yi Ya Jefa Rayuwarsu Cikin Hadari

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa ta bukaci kawo karshen zarge-zargen da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa ‘yan jarida Gaza na danganta su

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa ta bukaci kawo karshen zarge-zargen da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa ‘yan jarida Gaza na danganta su da ‘yan ta’adda.

kungiyar ta jaddada cewa: Rikicin da Isra’ila ke yi da kafafen yada labarai da danganta ‘yanjaridan Gaza da ‘yan ta’adda ya jefa rayuwarsu cikin hadari.

Dangane da haka, kwamitin tallafawa ‘yan jaridan Palastinawa ya yi Allah wadai da matakin da gwamnatin sahyoniyawan ta dauka na cin mutuncin ‘yan jaridun Falastinu tare da alakanta su da zargin ta’addanci maras tushe.

Har ila yau wannan komitin ya bayyana cewa: Matakin da gwamnatin sahyoniya ta dauka na tuhumar ‘yan jarida zai jefa rayuwarsu cikin hadari da kuma raunana amincewar jama’a ga kafafen yada labarai.

Kwamitin tallafawa ‘yan jaridan Falasdinawa ya jaddada cewa kamata ya yi gwamnatin sahyoniyawan ta kawo karshen farfagandar da ke da nufin lalata martabar ‘yan jarida tare da ba da damar gudanar da bincike mai zaman kansa na kasa da kasa kan kisan da suke yi a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments