Dakarun Hizbullah: Mun Dakile Duk Wani Yunkurin “Yan Sahayoniya Na Yin Kutse cikin Lebanon

Dakarun Hizbullah sun sanar da cewa sun dakile duk wani yunkurin ‘yan sahayoniya na yin kutse ta kasa cikin kasar Lebanon. Sanarwar da dakarun na

Dakarun Hizbullah sun sanar da cewa sun dakile duk wani yunkurin ‘yan sahayoniya na yin kutse ta kasa cikin kasar Lebanon.

Sanarwar da dakarun na Hizbullah su ka fitar a jiya Juma’a, sun ce bayan da abokan gaba su ka ci kasa wajen yin kutse ta dukkanin yankuna, sun koma wasu sabbin wuraren daga yamma, suna son shiga yankin “Ra;asu Naqurah” da “Jallul-Alam” da “Labunah” sai dai kuma shi ma sun sha kashi.

Gabanin kokarin yin kutsen, jiragen sama na HKI sun kai munanan hare-hare da kuma wasu hare-haren daga jiragen ruwa. Da su ka fara kokarin yin kutse, sun fuskanci mayar da martani mai tsanani daga mujahidai, lamarin da ya tilasta musu komawa inda su ka fito.

A ranakun Laraba da Alhamis, sojojin mamayar sun yi kokarin yin kutse amma duk sun fuskanci mayar da martani mai tsanani, lamarin da ya tilasa musu komawa da baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments