Birtaniya Ta Dakatar Da Sayar Wa Isra’ila Wasu Makamai

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa kasar ta dakatar da sayar wa Isra’ila wasu makamai. Matakin ya zo ne bayan kammala wani bincike kan ko

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa kasar ta dakatar da sayar wa Isra’ila wasu makamai.

Matakin ya zo ne bayan kammala wani bincike kan ko Isra’ila na bin dokar kasashen duniya kan tausaya wa dan’adam yayin yakin da take yi a Gaza, inji sakataren harkokin wajen Birtaniyar David Lammy.

Lammy, ya ce an dakatar da lasisi 30 na sayar da kayan yaki ga Isra’ila, wadanda suka hada da kunshi kayan aikin soji kamar jirage, da helikwafta, da jirage marasa matuka da ke ba da damar kai hari ta kasa.

Bayanin ya ce hadarin cewa an yi amfani da kayayyakin da aka sayar wa Isra’ilar a wajen da suka karya dokokin tausaya wa dan’adam.

Sai dai Birtaniyar ta ce binciken da suka yi ba ya nufin yanke hukunci kan shari’ar da ke gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

An jima da al’ummomin kasashen yamma ke zanga zangar bukatar ganin kasashen su sun daina goyan baya ko tallafin da suke baiwa Isra’ila ko kuma dakatar da sayar mata da makamai wadanda bayanai da dama suka nuna alamar tana amfani dasu a yakin da take a Gaza.

Bayanai sun nuna cewa wannan dakatarwar da Birtaniya ta yi na sayar wa Isra’ila makamai ya shafi lasisi 30 ne kawai daga cikin 350 na kayan yakin da take sayar wa Isra’ilar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments