Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana goyon bayansa ga hankoron Najeriya na samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
A yayin wata hira ta wayar tarho tsakaninsa da takwaransa na Nijeriya, Bola Tinubu, Biden ya bayyana aniyar inganta wakilcin nahiyar Afirka a tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Tattaunawar ta dace da muhawarar da ake ci gaba da yi game da wakilcin ƙasashen Afirka a Majalisar Dinkin Duniyar.
“Amurka na da aniyar ganin Afrika ta samu kujerun dindindin guda biyu a majalisar,” a cewarsa.
Fatan Nijeriya na samun kujerar dindindin na nuna dadaddiyar bukatar kara samun wakilci a harkokin gudanarwar duniya.
A halin yanzu, Afirka na da kujerun karba-karba guda uku a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniyar mai mambobi 15, yayin da a duk bayan shekaru biyu babban zauren majalisar ke zaɓar mambobin da ba na dindindin su biyar na wa’adin shekaru bibiyu.