Rahoton na hadin gwiwa a tsakanin Bankin Duniyar da kuma MDD, ya bayyana cewa; Rusau din da Isra’ila ta yi a Gaza, ya haddasa kudaden da sun kai Dalar Amurka biliyan 18.5
Rahoton wanda kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto a jiya Talata da dare, ya kuma ce kudaden da aka yi asara, suna daidai da kaso 97% na kudin shigar yammacin kogin Jordan da Gaza a shekarar 2022.
Gidajen da HKI ta rusa sun kai kaso 72% na jumillar gidajen yankin na Gaza. Sai kuma muhimman cibiyoyi irin su wuraren samar da ruwan sha, kiwon lafiya da makarantu da sun kai 19%, sai kuma kaso 9% na masana’antun yankin.
Sanadiyyar rusau din da akwai ton miliyan 29 na bola da ta taru a cikin yankin na Gaza.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoba ne na 2023 HKI ta fara kai hare-hare akan yankin Gaza da yi wa mazaunansa kisan kiyashi. Ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun haura 33,000, yayin da wani adadin da yah aura 75,000 su ka jikkata. Mafi yawancin mutanen da HKI take kashewa mata ne da kananan yara.