Shugaban jami’in diplomasiyyar Iran Ali Bakiri Kani wanda ya tattauna ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ahmad Ataf , ya bayyana cewa: Ya gargadi HKI akan aikin ta’addancin da ta yi na yi wa shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas kisan gilla.
Ali Akbar Bakiri ya kuma ce; Babu shakka cewa jamhuriyar musulunci ta Iran za ta yi aiki da hakkinta wajen ladabtar da HKI, kuma zai zama mai tasiri.
Babban jami’in diplomasiyyar na Iran ya kuma kara da cewa; Da akwai bukatar a yi wani taron gaggawa na kungiyar kasashen musulmi domin tattauna shahadar Isma’ila Haniyyah wanda zai sami halartar minstocin harkokin wajen.
A nashi gefen ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ahmad Ataf ta yaba wa Iran saboda bijiro taron gaggawa na kungiyar kasashen musulmi akan shahadar Isma’ila Haniyyah.
Haka nan kuma ministan na Aljeriya ya bayyana yadda al’ummar kasarsa da gwamnati suke yin tir da kisan gillar da HKI ta yi wa Isma’ila Haniyyah a kasar Iran,wanda teka hurumin daya ce daga cikin kasashen musulmi.