Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya taya zababben shugaban kasar Iran murna tare da bayyana shiri Majalisarsa na hadin gwiwa da sabuwar gwamnatin Iran
A cikin wata sakon wasika da ya aikewa zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya taya shi murnar zaɓen da aka yi masa a matsayin shugaban Jamhuriyar musulunci ta Iran, tare da bayyana shirinsa na gudanar da aikin haɗin gwiwa da sabuwar gwamnatin ta Iran.
Guterres ya bayyana farin cikinsa da zaben da aka yi wa Pezeshkian a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya kuma bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya da shi kansa na fatan yin aiki tare da sabuwar gwamnati a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi ishara da irin muhimmiyar rawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take takawa a yankin, inda ya yi kira da ta kara taimakawa wajen warware rikice-rikicen yankin da kuma hana barkewar sabbin tashe-tashen hankula da ka iya haifar da barazana a yankin da kuma wajensa.
Guterres ya kuma tabbatar da aniyar Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da bayar da goyon baya ga kokarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na cimma manufofin ci gabanta mai dorewa.