Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Falasdinawa suna rayuwa cikin jahannama don haka kada duniya ta wofantar da lamarinsu
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya kwatanta yanayin da Falasdinawa suke ciki tare da masifar da suke fuskanta tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, da “Jahannama da azabarta ke kara ta’azzara kowace rana.
Wannan ya zo ne a cikin jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis yayin wani taro a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York game da batun Hukumar Ba da Da Agaji da Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa a yankin Gabas ta Tsakiya{UNRWA}..
Guterres ya bayyana halin da ake ciki a Zirin Gaza da cewa ya wuce tunanin dan Adam. Ya ce: “Mun tozarta al’ummar Gaza, suna rayuwa cikin jahannama da masifu suke kara ta’azzara kowace rana.”